Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iran Zata Nazarci Tayin Da Javier Solana Ya Gabatar Mata, In Ji Ali Larijani


Iran ta ce akwai matakan kwarai a cikin sabon tayin da wasu kasashe suka gabatar mata da nufin lallashinta a kan ta kawo karshen shirinta na tace karfen Uranium.

Amma kuma babban jami’in shawarwarin nukiliya na kasar, Ali Larijani, ya ce akwai abubuwa da dama da aka bar su cikin duhu a wannan tayin da aka gabatar musu. Bai yi karin bayani ba, ya kuma ce Iran zata zauna ta nazarci wannan tayi dalla-dalla.

Larijani yayi magana ne a bayan tattaunawar sa’o’i biyu da babban jami’in hulda da kasashen waje na Kungiyar Tarayyar Turai, Javier Solana, kan wannan tayin sakawa Iran da alheri idan ta watsar da shirinta na nukiliya. Solana ya bayyana tattaunawarsu ta yau a zaman wadda ta yi ma’ana.

Jami’ai ba su fadi abinda ke kunshe a cikin wannan tayin da kasar Jamus tare da kasashe biyar masu kujerun dindindin a Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya (Amurka, Britaniya, Faransa, Rasha da Sin) suka tsara ba.

Jaridar New York Times da ake bugawa a nan Amurka ta ambaci wasu majiyoyin diflomasiyya su na fadin cewa a karkashin wannan tayi, za a kyale Iran ta sayi fasahar aikin gona daga Amurka, da kuma kayayyakin gyaran jiragen sama daga kamfanonin Airbus na Turai da Boeing na Amurka. Har ila yau tayin ya kunshi barazanar daukar matakan hukumta Iran idan ta ki yarda ta bayar da hadin kai.

XS
SM
MD
LG