Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mayaka Masu Kishin Islama A Somaliya Sun Dirkaki Birnin Jowhar


Mayakan sa kai masu goyon bayan akidar Islama a kasar Somaliya sun dirkaki birnin Jowhar, a bayan da suka kwace birnin Mogadishu a jiya litinin.

Shaidu sunce a yau Talata, mayakan sun kafa sansani a wani waje mai tazarar kilomita 20 a kudu da birnin Jowhar, su na jiran umurni domin su fara kai hari. Jowhar ita ce tunga guda daya tak da ta rage a hannun mayakan sa kai na tarayyar kungiyoyi masu kyamar cusa addini cikin harkokin mulki, wadanda suka yi yaki da masu akidar addinin Islama a Mogadishu.

A birnin Mogadishu, yau Talata daruruwan ‘yan kasar sun yi zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da fadawar birnin hannun mahukumtan Islama. Yawancin masu zanga-zangar ‘yan wani jinsin kasar ne mai suna Abgal wadanda suka jagoranci tawaye a kan masu akidar Islama a arewacin birnin Mogadishu.

Shugabannin kungiyoyin kawancen masu adawa da cusa addini a mulkin kasar sun dage cewar har yanzu ba’a kare yakin birnin Mogadishu ba suna masu cewa sojojinsu za su danna kai domin sake kwace yankin.

Jiya Litinin ne Kotunan Islama na birnin Mogadishu, suka ayyanar da samun nasara akan shugabannin tarayyar kungiyoyin mayakan sa kai bayan da mayakan sai kai masu biyayya ga kotunan suka kori mayakan masu kyamar addini a cikin mulki suka fita daga birnin.

XS
SM
MD
LG