Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Abu Musab al-Zarqawi


An kashe madugun 'yan gwagwarmayar kasar Iraqi, Abu Musab al-Zarqawi, a wani farmakin hadin guiwa da sojojin Amurka da na Iraqi suka kai.

Firayim ministan Iraqi, Nouri al-Maliki, shi ya bayyana mutuwar al-Zarqawi a lokacin wani taron manema labarai na hadin guiwa tare da kwamandan sojojin Amurka a Iraqi, Janar George Casey, da kuma jakadan Amurka, Zalmay Khalilzad.

Firayim ministan ya ce wasu mukarraban al-Zarqawi su bakwai sun mutu tare da shi a wani makwancinsu dake kusa da Baquba a arewa maso gabas da babban birnin kasar.

Janar Casey ya ce wasu manyan 'yan kungiyar al-Zarqawi ne suka fallasa inda yake. Kungiyar tana kai hare-haren kunar-bakin-wake kusan kullum a cikin shekaru ukun da suka shige. Janar Casey ya ce an tabbatar da cewar al-Zarqawi ya mutu a bayan da aka dauki hoton yatsarsa domin gwadawa da hoton da ake da shi, aka kuma ga tabon da aka sani a jikinsa tare da kamannin fuskarsa.

Kungiyar al-qa'ida a Iraqi ta tabbatar da mutuwar al-Zarqawi a wani sakon da ta buga a duniyar gizo inda ta ce yayi shahada.

Jami'an gwamnatin kasar Jordan sun ce hukumomin leken asirinsu sun bayar da gudumawa ga farmakin da ya kai ga kashe al-Zarqawi, haifaffen kasar Jordan. Kotunan kasar Jordan sun yankewa al-Zarqawi hukumcin kisa a bayan idanunsa dangane da kashe wani jami'in diflomasiyyar Amurka a shekarar 2002.

XS
SM
MD
LG