Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojin Amirka  a Iraq sun sake kai farmaki akan 'yan Alqa'ida


A yau Litinin rundunar sojin Amirka a Iraq ta ce sojojin kawance sun kai wasu hare hare ta jiragen sama a kusa da garin Baquba kuma ta kashe wasu ‘yan gwagwarmaya bakwai masu alaka da kungiyar Alqa’ida tare da wasu yara kanana biyu. Rundunar ta ce ‘yan gwagwarmayar suna da dangantaka da wani babban jami’in kungiyar kuma yana taimakawa sojojin haya da kungiyar ke dauka a wani wajen shakatawa.

Manjo Janar William Caldwell ya tabbatar cewa yaran biyu da aka samu daya dan watanni 6 da dan shekaru hudu da haifuwa, suna tare da ‘yan gwagwarmayar wadanda suka fara harbin sojoin Amirka. Ya bayyana kisan yaran a matsayin rashin sa’a. Yaro na uku kuma yaji rauni, tun dan kaishi jinya a Asibiti. Wannan sabon hari shine na bayan bayan nan da aka kai tun lokacin da rundunar ta kai harin da ta kashe shugaban Alqa’ida a Iraq Abu Musab Alzakawi a kusa da garin Baquba a makon jiya. Kungiyar ta Alqa’ida ta fada a cikin wata sanarwa da ta aike ta dandalin sadarwar Intanet a yau Litinin cewa ta nada Sheik Abu Hamza Al-Muhajer a matsayin sabon shugaban kungiyar.

XS
SM
MD
LG