Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush ya kai ziyarar ba zata Kasar Iraq


A yau Talata, Shugaba Bush na Amirka ya kai ziyara ba zata zuwa kasar Iraq kwana guda bayan da ya gana da manyan masu ba shi shawara ta fuskar tsaro kan irin rawar da Amirka za ta taka a kan makomar kasar Iraq. Fadar white House ta shugaban Amirka ta tabbatar cewa shugaban yaje kasar Iraq ne domin tattaunawa da firayi-ministan Iraq Nouri Al-maliki da kuma wasu jami’an gwamnatin Iraq. Kafin wannan ziyara tasa, ada ana jin shugaban zai tattauna ne ta hanyar video kai tsaye tare da shugabannin kasar Iraq a yau Talata daga gidan Hutunsa na KamDevit dake jahar Maryland kusa da binrin Washington DC.

Jiya Litinin Mr. Bush ya tattauna da jami’an gwamnatinsa akan yadda Amirka zata taimaki kasar Iraq ta shawo kan matsalolin tsaro, da tattalin arziki da hanyayin samun makamashi. Shugaba Bush ya lashi takwabin cewa Amirka zata ci gaba da kasancewa tare da kasar Iraq a daidai wannan lokaci da sabon ministan tsaron kasar yake kokarin nazarin halin da kasar take ciki. Duk da haka shugaba Bush yaki yayi hasashe akan ko yaushe sojojin Amirka za su fice daga kasar iraq.

Shugaba Bush ya kuma roki kasashe dake makobtaka da kasar Iraq su kara taimakawa kasar Iraq, a wajen kokarinta na sake gina kasar ya ce zai sake matsawa kasashen duniya da su ka yi alkawarin taimaka kasar da dala miliyon dubu da dari uku akan su cika alkawari. Duk da haka ya yi gargadin cewa magajin shugaban kungiyar alqa’ida a Iraq, musab Alzakawi zai shiga ayarin mutanen da amirka take nema ruwa a jallo domin hukunta shi. A makon jiya ne sojin amirka suka kashe alzakawi a wani hari da suka kai kan gidan da yake boye a ciki.

XS
SM
MD
LG