Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mayakan sa kai masu akidar Islama a kasar Somaliya sun kwace garin Jowhar


Mayakan sa kai masu akidar Islama a kasar Somaliya sun kwace garin Jowhar, gari na karshe da ke hannun shugabannin tarayyar kungiyoyi masu adawa da cusa addini a harkokin mulki wadanda ke samun goyon bayan Amirka.

Shedu sun ce mayaka masu goyon bayan kotutun Islaman kasar sun kwace garin da kuma filin saukar jiragen samansa a wani hari sa suka shiriya suka kai cikinsa a yau Laraba.

“yan kungiyar mayakan sakan Islaman sun ce akallan mutane 4 sun mutu kuma wasu 10 sunji rauni. Shugabannin tarayyar kungiyoyi masu adawa da cusa addini a harkokin mulkin sun yi kokari sake hada kai a garin Jowhar bayanda birnin Mogadishu ya fita hannunsu a makon jiya.

Mayan shugabannin tarayyar kungiyoyin 2 sun fice daga garin Jowhar jiya Talata sannan wani shugaban bangaren tarayyar Abdi Hassan Awale shi kuma ya kaurace musu ya koma hannun masu akidar Islaman.

Labarin yace biyu daga cikin shugabannin sun kama hanyarsu ta zuwa garin El Burr a tsakiyar kasar Somaliya a cikin wani a yarin motocin a-kori kura dauke da manyan bindigogi.

Mutane fiye da dari 3 da 50 ne suka rasa rayukansu a sakamakon fada tsakanin kungiyoyin tarayyar masu adawa da akidar islama a mulkin kasar da kuma masu goyon bayan kotunan kasar.

XS
SM
MD
LG