Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahukuntan jihar Ananbra dake kudancin Nigeria sun kafa dokar hana yawo


Mahukuntan jihar Anambra dake kudancin Nigeria sun kafa dokar hana yawo bayan barakar da ta barke tsakanin wata kungiyar ’yan tsagera da 'yan sanda.

Gwamna Peter Obi na jihar Anambra a jawabi ga al’umar Jihar ta gidajen Talabizin a jiya lahadi,ya kafa dokar hana fita,da kuma tura sojoji kan titunan birnin Anacha domin kawo karshen tashe tashen hankula da yanzu ya kai kwanaki hudu. Wani dan jarida Mike Mbonye, yace dokar hana fitan tana nan har zuwa Asabar yayinda gwamnati take kara tura dakaru zuwa birnin domin magance wannan fitina.Yace shugaba Obasanjo ne ya bada umurni daukan wannan matakan tsaro.

Wani hari da yan sanda su kai ranar alhamis ne ya janyo arangama tsakaninsu da magoya bayan kungiyar yan aware masu neman tabbatarda pallewar da kuma kafa kasar Biyafara, da akafi sani da MOSSOB. Akalla mutane shida ne aka kashe a arangamar da ta ci gaba har asabar dinnan,wadda ta sa hukumomi suka tura sojoji domin magance fitinar. Mbonye yace gwamnatin jihar ta fahimci cewa fitinar tafi karfin yan sanda.

Kungiyar yan awaren MOSSOB wadda shugabanta Ralph Uwazuruike ahalin yanzu yana tsare yana dakon shara;a bisa tuhumarsa da laifin cin amanar kasa, cikin shekarun 1990 ne ya soma kampen na neman pallewar kudu maso gabshin Najriya wadda akasarin mazauna yankin yan kabilar Ibo ne. Kungiyar tana da dumbin magoya baya cikin kabilar ibo,ana ganin wannan hari hukuma ta kaishine domin fige fukakan kungiyar dake kara bunkasa a yankin. Yan sanda sun kai hare hare a wurare da dama da ake zato yan kungiyar ke boye.

XS
SM
MD
LG