Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush ya tafi birnin Vienna domin taron kolin kungiyar kasashen yammacin Tekun Atlantika...


Shugaba Bush na Amurka yana birnin Vienna domin halartar taron shugabannin kasashen Kungiyar Tarayyar Turai da ake sa ran zai fi maida hankali akan shirin Nukiliyar kasar Iran, da ayyukan ta’addanci, da kuma cinikayya. Ana sa ran Shugabnnin kasashen Turai za su batun rufe gidan wakafin Amurka dake mashigin Ruwa na Guantanamo a kasar Cuba. Mai bada shawara ga shugaba Bush kan harkokin tsaro Stephen Hadley ya ce neman goyon baya da karfafa akidar demokradiyya, da nasara kan yaki da ta’addanci sune manya kan agendar jawabin shugaba Bush a wajen taron.

Taron zai sake nazarin kokarin manyan kasashen wajen warware rikicin Nukiliyar kasar Farisa, amma wakilin Muryar Amirka dake tafiya da shugaba Bush ya ce basa tsammanin wani muhimmin sanarwa game da wannan batu. Yanzu dai Farisa tana nazarin kayan rarrashinta dake da goyon bayan kwamitin Sulhu na MDD, da zai soma aiki da zarar ta daina tace ma’adinan Uranium.

Mr. Bush ya ce babbar barazana ce ga dukkan mutane idan Iran ta mallaki makaman Nukiliya,amma ya ce za ta ga falala mai yawa, muddin ta daina tace ma’adinan matakin da sai an tabbatarda shi tukuna.

XS
SM
MD
LG