Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Olusegun Obasanjo Ya Sake Yin Garambawul A Majalisar Ministocinsa


Shugaba Olusegun Obasanjo na Nijeriya yayi garambawul a majalisar ministocinsa, inda ministar kudi yanzu ta koma ma’aikatar harkokin waje.

Ngozi Okonjo-Iweala ta zamo ministar hulda da kasashen waje ta Nijeriya, yayin da mataimakiyarta, Menadi Usman, ta zamo ministar harkokin kudi. Shi kuma ministan hulda da kasashen waje mai barin gado, Oluyemi Adeniji, ya zamo minista mai kula da harkokin cikin gida.

Wannan garambawul na yau laraba shi ne na baya-bayan nan da gwamnati ta gudanar yayin da kasar ta doshi babban zabe a shekara mai zuwa.

A cikin wata gudan da ya shige, Cif Obasanjo ya maye gurbin wasu manyan hafsoshin soja uku tare da na mai ba shi shawara a kan harkokin tsaron kasa. Jami’an gwamnati suka ce wasu ministocin da dama sun bar kujerunsu domin su yi takarar wasu mukamai.

XS
SM
MD
LG