Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firimiya Wen Jiabao Na Kasar Sin Yana Afirka Ta Kudu


Firimiya Wen Jiabao na kasar Sin ya sauka a Afirka ta Kudu, zango na biyar a rangadin da yake yi na kasashen Afirka bakwai.

An shirya Mr. Wen zai yi tattaunawar kwanaki biyu tare da shugaba Thabo Mbeki na Afirka ta Kudu da kuma wasu shugabannin siyasa da na ’yan kasuwar kasar. Ana sa ran gwamnatocin biyu zasu rattaba hannu a kan yarjejeniyoyin cinikayya da yin amfani da makamashin nukiliya ta hanyar lumana.

Babban makasudin wannan rangadi na firimiyan shi ne karfafa huldar tattalin arziki a tsakanin kasar Sin da nahiyar Afirka.

JIya talata, Mr. Wen ya ziyarci kasar Angola, inda jami’an Sin suka rattaba hannu kan yarjejeniyoyin kara taimakawa Angola wajen farfadowa daga yakin basasar shekaru 27. Tun kafin nan, kasar Sin ta bai wa Angola rancen dubban miliyoyin daloli, yayin da ita Angola zata samarwa da kasar Sin man fetur.

Masu sukar lamiri sun zargi kasar Sin da kokarin wawushe albarkatun kasa na Afirka, amma kuma shugaba Jose Eduardo Dos Santos na Angola ya kare kasar Sin yana mai fadin cewa matakan da take dauka masu amfani ne ga dukkan bangarorin.

XS
SM
MD
LG