Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kofi Annan Yace Da Gaske Iran Tana Nazarin Tayin Da Aka Gabatar Mata


Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, MDD, Kofi Annan, ya ce yayi imani kasar Iran da gaske tana nazarin tayin da kasashen duniya suka gabatar mata da nufin warware rikicin da ake yi a kan shirinta na nukiliya.

Mr. Annan yayi wannan furuci a lokacin wani taron ’yan jarida alhamis a birnin Geneva, a bayan tattaunawar da yayi da ministan harkokin wajen Iran, Manouchehr Mottaki. Babban sakataren na MDD ya ce sun kuma tattauna a kan lokacin da Iran zata bayar da amsa kan wannan tayi, amma kuma ba a ambaci wata takamammiyar rana ba.

Jiya laraba, ministan harkokin wajen Iran ya fada cikin wata hira da gidan telebijin na Italiya cewa ba a tsayar da wata takamammiyar ranar bayar da amsa ba a lokacin da babban jami’in hulda da kasashen waje na tarayyar Turai, Javier Solana, ya gabatar da wannan tayi ga Iran cikin watan nan na Yuni.

Amma kuma shugaba Bush na Amurka ya ce shirin kasar Iran na bayar da amsa a karshen watan Agusta jan lokaci ne fiye da kima.

A halin da ake ciki, ministan harkokin wajen Italiya, Massimo D’Alema, wanda ya gana da takwaran aikinsa na Iran a birnin Rum, ya ce ba ya jin cewa kasar Iran tana dab da kera makamin nukiliya.

XS
SM
MD
LG