Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firayiminista Nouri Al-maliki ya saki daruruwan fursunoni


Daruruwan fursinoni na Iraqi ne aka sake a karkashin shirin ahuwa don kawo fahimtar juna da Friminista Nouri Al-maliki ya bayyana a ranar Lahadi da ta wuce. Kimanin fursinoni Dari Hudu da hamsin aka sake yau Talata, daga gidan wakafin Abu Gharaib da wasu daga gidajen sarka cikin sassan kasar. Mr. Maliki ya yi alkawarin zai sake mutane dubu biyu da dari biyar kamin karshen wannan wata. Yawancin wadanda aka saken ba wadanda ke da laifin aikata manyan laifuffuka bane, wasu kuma wadanda aka tsare bisa kuskure ne.

Ahalin yanzu kuma, rundunar sojin Amurka dake Iraq ta ce wasu hare haren 'yan gwagwar maya har biyu sun kashe sojinta biyu a wajen Bagadaza, sannan wani bam da aka da sa cikin mota a Kirkuk ya kashe 'yan Iraqin uku. Sa’o’i kadan bayan haka, wani bam din ya kashe mutane uku a unguwannin Dora a Bagadazan. A wata sabuwa kuma, babbar kotu ta musamman a Iraqin, ta tsaida 21 ga watan Agusta ranar da za’a soma shara’ar Saddam Husssein da manyan jami’ansa a zagaye na biyu, bisa zargin kisar gillar dubban kurdawa, cikin shekarun 1980 a garin Anfal.

XS
SM
MD
LG