Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firayi-ministan Isra’ila Ehud Olmert yaki yarda da  ‘yan kishin Palesdinu


Firayi-ministan Isra’ila Ehud Olmert yaki yarda da bukatar da kungiyoyin ‘yan kishin Palesdinu suka gabatar, wa’anda suka ce sai an biya su kafin su sako sojan nan na Isra’ila da suke garkuwa da shi, wanda suka bayyana niyyarsu na sakin nasa gobe Talata. Mr. Olmert yace ba wata yarjejeniyar da gwamnatinsa zata kulla da kowa don neman a sako wannan matashin sojan na Isra’ila, 19, mai mukamin Kofur wanda tun ran 25 ga watan jiya na Yuni aka sace shi. Mr. Olmert yace alhakin maido da sojan hannun Isra’ila cikin koshin lafiya yanarateye a wuyan su hukumomin na Palesdinu. P-ministan ya fayyace matsayin nasa ne bayanda kungiyoyi ukku na Palesdinu suka yi barazanar daukar wani matakin da basu fayyace ba akan sojan na Isra’ila, sai fa idan Isra’ila ta sako daruruwan ‘yan palesdinun dake gidajenta na kurkuku. Kakakin gwamnatin Palesdinu da Hamas ke jan ragamarta, Ghazi Hamad yace wadannan sharuddan sako sojan isra’ila din da kungiyoyin suka gitta kamar maida amsa ne ga hare-haren jiragen sama da Isra’ila ke ta kaiwa akan Zirin Gaza ne a kwannakin nan.

XS
SM
MD
LG