Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firayi ministan Somalia Ali Mohammed Gedi yace Osama Bin Laden ya girka mutanensa a  Somalia


Firayi ministan Somalia Ali Mohammed Gedi yace madugun al-Qaida na duniya Osama Bin Laden ya girka mutanensa a sassan Somalia daban-daban, da niyyar jefa kasar cikin wata sabuwar fitina. A jiya da marece ne p-ministan yake wannan zargin, kwana guda bayan wani samon kaset da shi OBL ya aikawa duniya, inda yake jan kunnen kasashen duniya da kada su kuskura su aika sojansu zuwa can Somalia.

A tadin da yayi da manema labarai, Mr. Gedi yace Osama bin Ladin ba wani shaihin malami bane, kuma baya da wani tasiri akan Somalia. Sai dai kuma an san cewa shi kansa p-minista Gedi, tashi gwamnatin kamar hoto ce don in bayan cikin garin Baidoua da take zaune, kusan bata da wani tasiri a duk Somalia. Haka shima shugaban kungiyar kotunan Somalia dake rike da kasar a yanzu, Shiekh Sharif Ahmed ya nisanta da kansa daga wannan kalamin na Osama Bin Ladin, koda yake kuma yace Osama Bill Ladin yana bayyana ra’ayinsa ne kawai kamar kowane shugaba na kasa da kasa.

XS
SM
MD
LG