Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin mamatan fashewar  cikin jiragen kasa a Indiya ya karu


Adadin wadanda suka mutu a wata fashewa da ta auku cikin wani jirgin kasa a birnin Bambay dake yammacin kasar Indiya ya kai mutum 130, sannan mutane wajen 300 sun ji rauni. ‘Yan sanda sun ce fashe-fashen sun auku ne bi da bi a yau Talata da Yamma a dai-dai lokacin da ma’aikata suka tashi daga aiki, sunce wannan fashewar wani hari ne da aka shirya aka kai a jere kan jiragen kasan.

Ya zuwa wannan lokaci dai ba wanda ya fito ya lashi takwabin cewa shine da alhakin kai hare-haren to amma ana jin cewa musulmi ‘yan aware dake yaki da gwamnatin kasar Indiya domin neman ‘yancin yankin Kashimir ne suka kai harin. Ana zama cikin shirin ko ta kwana a yawancin manyan biranen kasar Indiyan kuma mahukunta sun yi kira da a kwantar da hankali. Bayan wani taron gaggawa da majalisar ministocin kasar su ka yi, ministan harkokin cikin gidan kasar Indiya Shivraj Patil ya bayyana anniyar gwamnatin kasar ta yaki da ayyukan ta’adaddanci. Tun da fari kamfanin dillancin labarum Associated Press ya ambaci Mr. Patil yana mai cewa mahukuntan kasar sun sami labarin cewa za’a kai wannan harin to amma ba su san ko yaushe ne ko kuma a ina za’a kai harin.

XS
SM
MD
LG