Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kakakin Majalisar Dinkin Duniya ya ce lokaci yayi da za'a sake tura sojojin Kiyaye zaman Lafiya ayari na biyu mai karfi a Kudancin Lebanon..


Kakakin Majalisar Dinkin Duniya Koffi Annan ya ce da akwai yiwuwar tura wani ayarin sojokin Kiyaye zaman lafiya na Majalisar wanda zai sassauta yakin da ake yi a yankin kudancin kasar Lebanon tsakanin Isra'ila da 'yan Hezullah.

Da yake jawabi ga Manema labarai na hadin guiwa tsakaninsa da shugaban Hukumar gudanarwar kasashen Turai, Jose Manuel Borroso, kakakin MDD Koffi Annan ya ce wani gagarimin a yarin sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD shine kadai zai iya taimakawa a sami zaman lafiya a wannan yankin na kudancin Lebanon inda mayakan sa kai na Hezbullah suke musayar wuta tsakaninsu da Isra’ila. Ya yi kira ga kasashen Turai da sauran gwamnatoci da su bada gudunmawar su na sojoji wadanda ya ce suke da kayan aikin mai yawa da kuma yawansu fiye da dubu biyu da MDD ta tura yankin a yanzu haka.

Wannan yankin yana bukatar matakin hanzari don haka wajibi ne kasashen duniya su tashi tsaye domin kawo karshen wannan fadar da kashe kashen mutane da ake yi a yankin. Sannan kuma yayi kira da a samo mataki mai dorewa da zai kawo karshen rikicin. Kasashen Turai masu yawa sun bayyana goyon bayansu ga irin wannan mataki na tura sojin kiyaye zaman lafiya na MDD, sannan Isra’ila kuma tana nuna shakku da dari dari game da wannan matakin, Amirka kuma bata ganin cewa tura Karin sojojin kiyaye zaman lafiya na iya hana ‘yan Hezbullah kai hare hare.

Su kuma masu fashin bakin al’amarin cewa su ka yi tura sojojin kiyaye zaman lafiyar na iya dakile kokarin da Isra’ila ta keyi na ganin ta tarwatsa gungun ‘yan Hezbullah wadanda ke rike da ikon yankin kudancin Lebanon.

Jawabin da Mr annan ya yi a birnin Brussell din ya hada da wani kokari na samun zaman lafiya a wani yanki da yaki ya daidai ta watau yankin Darfur na kasar Sudan. MDD ta jima tana matsawa gwamnatin kasar Sudan akan ta bada izini a tura sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD domin su maye gurbnin sojojin Kungiyar Tarayyar kasashen Afirka dake fama da rashin isasshen kayan aiki dake yankin ayanzu haka. Mr. Anan ya ce yana fata daga karshe dai mahukuntan kasar Sudan zasu bada izini a tura sojojin MDD yankin. Ya ce sunyi nisa ainun a shirye shiryensu da kuma kokarinsu na tura sojoji zuwa yankin Darfur kuma ya tattaunawa sosai da mahukuntan kasar Sudan inda suke neman hadin kansu su ba MDD izini ta tura sojojin yankin Darfur.

MDD da kungiyar Tarayyar Turai da wakilan kasar sudan da Amirka suna tattaunawa a birnin Brussell don samo hanyoyin samar da kudade da za’a ci gaba da barin sojojin kungiyar tarayyar Afirka a kasar na wasu watanni nan gaba.

XS
SM
MD
LG