Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila ta ce ba zata kara yawan sojojinta na kasa a lebanon ba


Kafofin yada labarun Isra’ila sunce majalisar ministocin tsaron kasar ta yanke shawara ba zata kara yawar sojojinta na kasa dake yaki da Helzullah a kasar Lebanon ba. Jami’an Isra’ila sunce firyiminista Ehud Olmert ya fadawa majalisar jami’an gwamnatinsa cewa sun cimma nasarar da suke bukata. Ministocin sun amince akan za su ci gaba da matsawa da kai hare hare ta sama sannan su takaita kai hari ta kasa a cikin kasar. Mr. Olmert ya gana da ministocin nasa a yau Alhamis kwana guda bayanda Isra’ila ta yi asarar sojojinta mafi yawa a rana guda tunda aka fara wannan yakin fiye da makonni biyu da suka wuce.

Jiya laraba an kasha sojojin Isara’ila tara sannan an jiwa 25 rauni a wata fada da suka gwabza a garin Bain Jbail inda Helbullah take da tunga mai karfi. Sojojin Isra’ila sunyi ta aman wuta a kudancin Labanon. An kashe ‘yan kasar Lebanon akalln uku. Kuma Hezbuyllah ta harba rokoki zuwa cikin kudancin isra’ila ta harbi gine gine. Wani jerin rokoki akai akai kuma sun sauka a garin Kiryat Shimona inda suka lalata wata masana’anta.

A halin yanzu kuma ministan shari'ar Isra’ila Haim Ramon ya ce taron kasa da kasa da aka tashi jiya laraba a birnin Rome, wanda aka tashi baram baram, ba tare da cimma wata yarjejeniyar tsagaita bude wuta ba, ya baiwa kasar isra’ila damar ci gaba da kai hare hare.

XS
SM
MD
LG