Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministocin harakokin wajen kassashen Larabawa suna wani zaman taron gaugawa yau a Beirut


Ministocin harakokin wajen kassashen Larabawa suna wani zaman taron gaugawa yau a Beirut domin karfafa shawarar da Lebanon ta bada na dasa aya ga tashin hankalin da ke wakana tsakanin Isra’ila da Hezbollah.

Ana sa zuciya ministocin za su tatauna kan shawarwarin da za su gabatar a wajen taron kolin Larabawa da za a yi kwanaki masu zuwa, tana yiwuwa a yi taron a Mecca babban birinin kasar Saudi Arabia.

Gwamnatin Lebanon na neman kawo sauyi ga daftarin MDD da ya bukaci tsagaita wuta. Gwamnatin Beirut na so ne kudurin ya bukaci Isra’ila ta janye dakarun ta daga Lebanon.

Kassashe biyar mambobin Commitin sulhu masu kujera dindin a MDD wanda suka hada da Amurika, Britaniya, Faransa, Rasha da China za su yi taro yau a New York domin nazari kan bukatar ta Lebanon.

Kakakin offishin Ministan harakokin wajen Isra’ila, Yigal Palmor ya ce, Isra’ila ta yi amanna da cewar aika dakarun kiyaye zaman lafiya cikin kudancin Lebanon ne kadai zai kawo karshen tashin hankalin.

XS
SM
MD
LG