Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya ta soma janye sojojinta daga mashigin rowan Bakassi


Najeriya ta soma janye sojojinta daga mashigin rowan Bakassi,gabannin wa’adi da MDD ta bayar na mika yankin ga kasar Kamaru.

Brigadier General Felix Chukuma yace dukkan sojojin Najeriya dubu 3 dake mashigin rowan zasu bar makuridn cikin mako mai zuwa.Amma yace Najeriya zata ci gaba da gudanarda harkokin mulki cikin yankin na shekaru biyu.

Najeriya da kamaru sun cimma yarjejeniya ta MDD cikin watan Yuni,bayan sun sha ringimu na shekaru fiyeda goma.

XS
SM
MD
LG