Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan siyasar kasar Togo suna shirin hada kai...


A jiya Laraba Mayan yan siyasar kasar Togo sun sake ganawa a rana ta biyu a birnin Ougadougou na kasar Burkina Faso shugabannin adawar kasar Togo sunce ayanzu dukkansu sun amince akan ayi zaben ‘yan majalisar dokokin kasar ba tare da bata lokaci ba, kuma ya kamata a bada sanarwar ranar da za’ayi zaben nan da ‘yan makonni kadan masu zuwa. Ita dai kasar Togo ta fada cikin rudanin siyasa bayan da akayi zaben shugaban kasa a watan Afirilu na shekarar bara zabenda tashe tashen hankula da zargin magudi suka dusashe.

Leopold Nigninvi na jam’iyar DCAP Democratic Convention for African People ya ce yana son ganin an sami makamar warware wannan rikici baki dayansa. Ya ce magoya bayansa sun san zurfin irin matsalar da kasar Togo take fuskanta. Don haka yace suna son kirkiryo yanayin da zai baiwa‘yan kasar damar zuwa kada kuri’unsu ba tare da tsoro ba.

Wakilin shugaban kasar Togo Foor Nagsinbe a zauren taron, ya ki yin jawabi, sai dai ya ce suna jiran babban dan Adawar kasar Gil Christ na jam’iyar Union of Forces for Change ya furta tukuna. Ana sa rai ayau Alhamis zai bulla zauren taron. Gwamnatin kasar Burkina ce ta kira wannan taron tattaunawar. Ministan tsaron kasar Jibril Bassolet ya ce taron yanada alfanu sosai. Sannan ya ce yanayin zauren wannan taro yanada kyau sosai, akwai alamar gamsuwa a fuskokin masu taron kuma yana jin cewa mashawartan zasu iya tsaida shawara kan wata hanyar warware rikicin kasar da zata dacewa kowa a kasar.

Rundunar sojin kasar Togo ce ta nada shugaban kasar lokacin da mahaifinsa Gnassigbe Oyadeima wanda ya shugabanci kasar na tsaron shekaru 38 ya mutu a watan fabarairun shekara data wuce. Mr. Gnassingbe ya gudanar da zaben shugaban kasar a kasar sannan ya ci zabe to amma abokan adawarsa sun yi zargin cewa anyi magudi a zaben. Dubban ‘yan gudun hijira ne suka arce daga Togo bayan da akayi zaben saboda fargabar tashin hankali. Akasarinsu basu koma gida ba har yanzu.

XS
SM
MD
LG