Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kakakin MDD Kofi Annan ya ce zai dau lokaci kafin a tura sojojin kiyaye zaman lafiya Lebanon


Kakakin MDD Kofi Annan ya ce mai yiwuwa ne tura sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD a kudancin kasar Lebanon ya kai makonni ko watanni nan gaba. Jiya Talata ce Mr. Annan ya fadawa gidan Talbijin na Isra’ila cewa kasashen duniya suna kokarin shirya ayarin soja da za’a tura yankin ba tare da bata lokaci ba. Anan birnin Washinton kuma kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amirka Sean MC Cormack ya ce ba zaiyiwu a ce sai bayan watanni za’a tura sojojin kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa zuwa yankin na Lebanon ba. Ya ce yakatama da kara hanzari wajen kamala shirye shiryen tura sojojin. Jami’an kasar Lebanon sunce za’a tura sojojinsu da na kiyayye zaman lafiya na kasa da kasa zuwa yankin kudancin Lebanon nan da ‘yan kwanaki. Rundunar sojan Isra’ila tana janyewa daga kasar Lebanon a daidai lokacin da shirin tsagaita bude wuta tsakaninta da mayakan Hezbullah yake aiki.

Amirka ta soki kasashen Iran da Syria da kakkausar harshe.

A halinda ake ciki kuma gwamnatin shugaba Bush jiya Talata ta yiwa kasashen Iran da Syria suka da kakkausar harshe bisa ikrirarin samun nasarar Hezbullah a rikicin kasar Lebanon. Mataimakin firayi ministan Isra’ila Shimon Peres wanda a halin yanzu ya gana da sakatariyar harkokin wajen Amirka Condelisa Rice ya ce watakila Hezbullah ta yi asaran kusan rabin sojojinda ba zuwa bakin daga.

XS
SM
MD
LG