Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar ’yan yakin sa kan Nigeria ta yankin Niger Delta mai arzikin mai tace an kashe mata mayakan akalla guda goma


Ƙungiyar ’yan yaƙin sa kan Nigeria ta Movement for the Emanicipation of the Niger Delta a yankin Niger Delta mai arzikin mai tace an kashe mata mayakan aƙalla guda goma a arangamar da suka yi da sojojin Nigeria.

Ƙungiyar tace a jiya lahadi da dare sojoji suka kaiwa yan ƙungiyar hari a jihar Bayelsa. Ƙungiyar tace an fafata ne a yayinda mayaƙan ke kokarin sako ma’aikacin kamfani mai na Shell da suka sace a kwanan nan. Kamfani mai na Shell ya tabbatar da cewa a ranar takwas ga wannan wata an sace wani ma’aikacinsa a Bayelsa.

Idan ba’a mance ba a makon jiya shugaba Obasanjo ya ce ba zata saɓu ba bindiga a ruwa, lokacinda ya bada sanarwar cewa za’a murkushe yan tawayen bayan da aka yi ta sace ma’aikatan mai. A shekaranjiya asabar rundunr sojan Nigeria tace ta kama fiye da yan yaƙin sa kai ɗari a sumamen da soja suka kai.

XS
SM
MD
LG