Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firayi ministan Lebanon ya roki Amirka data  ribanya taimakon da ta  keyi..


Firayiministan Lebanon Faoud Seniora ya yi kira ga Amirka data kara taimako da take baiwa kasrsa domin sake gine kasar bayanda yakin wata guda tsakaninta da Isra’ila da mayakan Hezbullah ya wargaza kasar. Jiya laraba ne firayiministan Labanon din ya roki shugaba Bush na Amirka akan ya kara matsawa isra’ila lamba domin ta daina kawanyar da ta kewa kasar Lebanon. Haka kumaya roki sauran kasshen duniya akan su kara taimakon kasar da kudi da kuma diplomaisyya. Isra’ila kuwa ta ce zata ci gaba da toshe duk hanyoyin shigar kasar Lebanon ta sama ko ta jiragen ruwa ko ta kan iyakarta da kasar Syria. Ministan harkokin wajen Syria Walid Mualem ya fadawa takwaran aikinsa na kasar Finland Erkki Tuomioja jiya Laraba a birnin Helsinki cewa Syria zata rufe kan iyakarta da Lebanon idan aka tura sojojin kiyaye zaman lafiya acan.

XS
SM
MD
LG