Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Rajin Zaman Lafiya Sun Yi Zanga-Zanga A Fadin Duniya...


'Yan rajin zaman lafiya sun gudanar da zanga-zanga a sassa dabam-dabam na duniya domin goyon bayan kara azamar kawo karshen tashin hankali a yankin Darfur na kasar Sudan.

Kungiyoyin kare hakkin bil Adama, cikinsu har da "Amnesty International" sun ayyana jiya lahadi a zaman ranar tunawa da Darfur a Duniya, sun kuma gudanar da gangami a kasashe fiye da talatin.

An gudanar da gangami guda a kofar ofishin jakadancin Sudan a London, daga bisani kuma aka gudanar da taron du'a'i a kofar gidan firayim minista Tony Blair na Britaniya.

Tun da fari, Mr. Blair ya bayar da rubutacciyar sanarwa inda yayi kira ga shugabannin Tarayyar Turai da su matsa lamba a kan shugabannin gwamnatin Sudan da na 'yan tawaye a kan su kawo karshen wannan yakin basasa.

Firayim ministan na Britaniya ya ce idan har Sudan ta yi na'am, to ya kamata kasashen Tarayyar Turai su shirya domin bayar da agajin kudi da yafewa kasar basussuka domin ta samu sukunin sake gina kasa.

Mr. Blair ya ce tilas ne Sudan ta yanke shawara cikin lokaci, yana mai fadin cewa idan har ta kasa daukar matakin kawo karshen rikicin Darfur to ya kamata kasashen Tarayyar Turai su mayar da ita saniyar ware.

XS
SM
MD
LG