Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Yi Juyin Mulki A Kasar Thailand


Sojoji a karkashin jagorancin janar Sondhi Boonyaratglin sun mamaye wasu cibiyoyi jiya talata da maraice a kewayen birnin Bangkok. Jami’an soja sun ce sun kwace gwamnati, sun soke yin aiki da tsarin mulki, sannan sun rufe akasarin cibiyoyin gwamnati.

Sojojin sun ayyana yau laraba a zaman ranar hutu, suka rufe bankuna da kasuwar hada hadar hannayen jari da makarantu.

A yayin da aka kaddamar da wannan juyin mulki, firayim minista Thaksin Shinawatra, wanda yake halartar zaman babban zauren taron Majalisar Dinkin Duniya a New York, ya ayyana dokar-ta-baci a babban birnin. Bangkok. Har ila yau ya kori janar Sondhi daga kan mukaminsa.

Shugabannin juyin mulkin sun yi watsi da wannan umurni na firayim ministan, suka gabatar da wata sanarwa a telebijin, inda suka roki jama’a da su kwantar da hankulansu. Wani kakakin shugabannin juyin mulkin ya ce sun dauki wannan matakin ne a saboda rarrabuwar kawuna sosai a kasar, ya kuma yi kira ga sauran sojoji da su kasance a cikin barikokinsu.

Jami’in ya ce an soke tsarin mulki na 1997, kuma kasar zata rungumi tafarkin dimokuradiyya bisa jagorancin sarki Bhumipol Adulyadej. Amma kuma babbar majalisar bayar da shawara ga sarkin, da kuma kotuna zasu ci gaba da gudanar da ayyukansu.

Firayim minista Thaksin ya soke jawabin da yayi shirin gabatarwa a zauren babban taron Majalisar Dinkin Duniya. Ba a san ko sojoji zasu kyale shi ya koma Thailand, ko kuma lokacin da hakan zai yiwu ba.

Thailand ta fuskanci juyin mulki ko yunkurin haka har sau 18 tun lokacin da ta zamo mulukiya a 1932.

Juyin mulkin na jiya talata shine sakamakon tankiyar da ta yi zafi a tsakanin hafsoshi masu goyon bayan janar Sondhi da masu biyayya ga firayim minista Thaksin.

Tankiyar siyasa ta yi ta karuwa a Thailand cikin shekara guda da ta shige a yayin da aka yi ta zanga zanga a kan tituna ana kira ga Mr. Thaksin da yayi murabus bisa zargin zarmiya da yin amfani da iko ta hanyar da ba ta dace ba. Firayim ministan ya kira zabe a watan Afrilu amma jam’iyyun adawa sun kaurace. daga baya kotu ta soke sakamakon zaben aka kuma shirya gudanar da zabe a wata mai zuwa. Kwanakin baya hukumar zabe ta nuna alamun cewa za a dage zaben zuwa watan Nuwamba. A yanzu dai babu tabbas a kan ko yaushe ne za a yi zabe.

Mr. Thaksin mai shekaru 57 da haihuwa, tsohon jami’in ’yan sanda ne, kuma dan kasuwa. An fara zabensa firayim minista a 2001, aka kuma sake zabensa a shekarar da ta shige.Wasu masu fashin baki sun ce suna tsammanin da yawa daga cikin masu karfin hali a birane zasu yi marhabin da wannan juyin mulki. Amma kuma har yanzu Mr. thaksin yana da farin jini sosai a wurin talakawa da mutanen karkara wadanda suka ci moriyar manufofinsa na rage kudin kiwon lafiya, da samar da rance maras tsada da kuma kudade masu yawa da ya ware domin ayyukan raya karkara.

Amurka ta ce tana sa idanu a kan lamarin, ta kuma yi kira ga al’ummar Thailand da su kwantar da hankulansu.

XS
SM
MD
LG