Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Majalisar Dokokin Iraqi Sun Bayar Da Sanarwar Samun Gagarumin Ci Gaba A Kokarin Warware Wasu Muhimman Batutuwa Biyu


'Yan majalisar dokokin Iraqi sun bayar da rahoton samun ci gaba a kokarin warware wasu muhimman batutuwa guda biyu wadanda suka rarraba kawunan majalisar. 'Yan majalisar sun ce a yau litinin zasu kafa wani kwamitin da zai nazarci bukatun ’yan mazhabin Sunni na sake yin gyara ga tsarin mulki, tare da biyan bukatun ’yan Shi’a na kafa musu yanki mai cin gashin kai a kudancin kasar.

A wani abinda ake ganin a zaman sasantawa ce tsakanin sassan biyu za a sake nazarin tsarin mulkin Iraqi domin ko za a yi masa gyara kamar yadda ’yan Sunni suka nema. Haka kuma za a nazarci kafa tsarin mulki irin na tarayya, inda a wannan makon ma ake sa ran gabatar da wani kudurin kafa yankuna masu cin gashin kai na manyan kabilu da mazhabobin kasar Iraqi, ciki har da yankin ’yan Shi’a mai cin gashin kai a lardunan kudancin kasar masu arzikin man fetur.

Da ma dai yankin arewacin kasar na Kurdawa tamkar mai cin gashin kai yake a yanzu haka.

Yarjejeniyar ta tanadi cewar duk wata dokar da za a kafa ta bullo da tsarin tarayya zata fara aiki ne watanni 18 bayan an zartas da ita.

A lokacin da yake magana a cikin wani shirin gidan telebijin na CNN, shugaba Jalal Talabani na Iraqi ya yaba da ci gaban da aka samu a majalisar dokokin a zaman shaidar cewa kasarsa tana iya kaucewa yakin basasa.

A can wani gefen kuma, tashin hankali a Bagadaza da wasu wuraren yayi sanadin mutuwar mutane akalla 21 a jiya lahadi. Jami’an Amurka sun ce an kashe sojojin kundumbala na Amurka su biyu a fada a lardin al-Anbar, yayin da aka gano karin gawarwaki a babban birnin kasar.

XS
SM
MD
LG