Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tarayyar Turai Ta Bayar Da Kudi Dala Dubu Dari Shida Domin Bin Sawun Murar Tsuntsaye A Nijeriya


Kungiyar Tarayyar Turai ta samar da tsabar kudi har kusan dala dubu 700 ga Hukumar Abinci da Aikin Gona ta Majalisar Dinkin Duniya, domin bincikowa da bin diddigin cutar murar tsuntsaye a Nijeriya. Wakilin Muryar Amurka Gilbert Da Costa, ya ce makasudin wannan aikin bincike shine murkushe wannan cuta baki dayanta daga kasar da ta fi kowacce yawan jama’a a nahiyar Afirka.

Wannan shiri na watanni shida ya kunshi nazari sosai a kan bulla, da yaduwa da kuma illar murar tsuntsaye a Nijeriya, da nufin kawar da wannan cuta daga kasar da ta fi kowacce yawan jama’a a Afirka.

Ma’aikatan lafiya su fiye da metan zasu karade fadin kasar suna binciken bulla ko yaduwar cutar.

An fara gano kwayar halittar cutar murar tsuntsaye jinsin H5N1 cikin watan Janairu a tsakanin kaji a Jihar Kaduna dake arewacin kasar, daga nan ta yadu cikin sauri zuwa jihohi 13 tare da babban birnin tarayyar kasar. Jami’an Nijeriya suka ce a yanzu dai an shawo kan yaduwar cutar, amma kuma kwararru na kasashen waje sun ce har yanzu ba a san ainihin tsanani na wannan matsalar ba.

Wakilin Hukumar Abinci da Aikin Gona ta MDD a Nijeriya, Helder Muteai, ya ce sanya idanu da bin diddigin zai taimaka wajen tabbatar da iyakar yaduwar cutar murar tsuntsaye a Nijeriya, yana mai cewa, "...akwai jihohi kimanin 14 da kuma Abuja, babban birnin tarayya, wadanda suka bayar da rahotannin bullar murar tsuntsaye. Amma kuma babu wanda ya san yawan yaduwar cutar a Nijeriya. Mun dai san cewa akwai yankunan kananan hukumomi kimanin 40 wadanda aka samu cutar a cikinsu."

Nijeriya, kasar Afirka da ta fara gano jinsin cutar mai kisa, H5N1, ba ta samu rahoton wani mutum ko guda da ya kamu da cutar ta murar tsuntsaye ba. Amma kuma akwai fargabar cewa dadewar kwayar cutar a Nijeriya zata kara kasadar yaduwarta zuwa jikin bil Adama, kamar yadda Dr. Muteai ya yi karin haske da cewa "...a Afirka tilas ne muyi hattara a saboda dangantakar kut da kut dake tsakanin dan adam da tsuntsaye, musamman a yankunan karkara inda a wasu lokutan dabbobi ke kwana cikin gida ko daki guda da mutane. Wannan lamari ne mai hatsari. Wannan shi ya sa tilas mu dauki lamarin da muhimmancin gaske a Nijeriya."

Kwayar halittar cutar murar tsuntsaye jinsin H5N1 tana harbin mutanen da suka kusanci tsuntsayen da suek dauke da ita. Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya ta ce mutane 247 suka kamu da kwayar cutar tun 2003, kuma akalla 144 daga cikinsu sun mutu.

XS
SM
MD
LG