Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Nigeria, ‘Yan tawaye sun kashe masu gadi biyu suka kuma sace baki ‘yan kassashen waje  guda biyar


Jammi’an masa’antun mai a Nigeria suka ce, ‘yan tawaye sun kashe masu gadi biyu suka kuma sace baki ‘yan kassashen waje guda biyar a jiya Talata, a cikin sace sacen mutane na baya baya nan da ya wakana a kudancin kasar mai arzikin man petre. Suka al’amarin ya wakana ne a garin Eket cikin yankin Niger Delta. Rahotanni na cewa, wadanda aka aka sacen sun hada da ‘yan kasar Britaniya uku.

A ranar Litinin, ‘yan tawaye sun sace ma’aikatan mai guda 25. Kampanin mai na shell, wanda ya dauki ma’aikatan aiki, ya ce, yau Laraba aka sako mutum na karshe daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su. Gungun ‘yan aware daga cikin yankin, suka ce su ke da alhakin sace mutanen, suka ce gurin su na yi hakan shi ne a saki shugaban kungiyar su Mujahid Dokubo Asari.

XS
SM
MD
LG