Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Sin Ta Yarda A Ladabtar Da Kawarta Koriya Ta Arewa A Majalisar Dinkin Duniya


Kasar Sin ta yarda cewar a hukumta kawarta Koriya ta Arewa a saboda ta gudanar da gwajin makamin nukiliya. Wakilin Muryar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya (MDD), Peter Heinlein, ya aiko da rahoton cewa Kwamitin Sulhun majalisar yana tattauna wata shawarar da Amurka ta gabatar ta kafa takunkumi mai tsauri a kan Koriya ta Arewa.

Jakadan kasar Sin a MDD, Wang Guangya, ya ce kasarsa zata goyi bayan bukatun Amurka da Japan na daukan matakan ladabtar da Koriya ta Arewa, yana mai cewa, "...ina jin cewa tilas ne a dauki wasu matakan ladabtarwa, amma tilas ne irin wadannan matakai su zamo wadanda suka dace."

A can baya, kasar Sin ta nuna dari-darin kyalewa a sanya takunkumi a kan makwabciyarta, kuma jakada Wang bai fadi irin matakin ladabtarwan da Sin take ganin ya dace ba. Amma kuma yayi nuni da cewa matakin ba zai yi tsaurin matakan da Amurka da Japan suke son a dauka na binciken dukkan kayayyakin dake shiga ko fita daga Koriya ta Arewa, tare da haramta sayar mata da dukkan makamai ba.

Wakilan Kwamitin Sulhun MDD sun yi tarurruka da dama bisa fatar cimma matsaya da sauri a kan kudurin takunkumi. Jakadan Amurka a MDD, John Bolton, ya ce ra’ayi ya zo guda a tsakanin wakilai 15 na kwamitin kan bukatar daukar mataki cikin gaggawa.

Kasar Japan, wadda take shugabancin Kwamitin Sulhu a wannan watan, ita tana so ne a dauki matakan ladabtarwa masu tsauri fiye da wadanda Amurka take nema. Jakadan Japan a MDD, Kenzo Oshima, ya ce duk da cewa kowa na so a gaggauta daukar wani mataki dangane da gwajin na Koriya ta Arewa, tilas ne a tuntubi juna sosai tare da yin shawarwari kafin a ce za a jefa kuri’a a kan kudurin takunkumi.

A halin da ake ciki, wata girgizar kasa mai karfi ta jijjiga arewacin Japan yau laraba da asubahi, har ma wasu mutane suka fara tunanin ko Koriya ta Arewa ta gudanar da gwajin nukiliya na biyu ne. Jim kadan a bayan wannan, Amurka da Koriya ta Kudu da kuma Japan duk sun ce babu wani bayanin da aka samu da zai tabbatar da cewa Koriya ta Arewa ta sake gwajin wani makamin na nukiliya.

XS
SM
MD
LG