Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Kotu Ta Musamman A Nijeriya Ta Fara Shari'ar Mataimakin Shugaba Atiku Abubakar


A jiya talata wata kotu ta musamman a Nijeriya ta fara sauraron karar da gwamnatin tarayya ta shigar tana tuhumar mataimakin shugaba Atiku Abubakar da laifin zarmiya. Wakilinmu Gilbert da Costa ya ce wannan tuhuma da ake yi wa Atiku Abubakar, ba zata rasa nasaba da rigimar dake tsakaninsa da shugaba Olusegun Obasanjo ba, wadda ta kara yin muni lokacin da shi Atiku Abubakar ya jagoranci gangamin murkushe shirin Tazarce a farkon shekarar nan.

Ana tuhumar mataimakin shugaba Atiku Abubakar da laifin yin rub da ciki a kan kudaden gwamnati tare da batar da sawun kudaden haramun. Atoni janar ne ya shigar da karar a madadin gwamnatin tarayya. Gwamnatin ta yi zargin cewa an wawure kudade kimanin dala miliyan 135 dake cikin asusun wata hukumar gwamnati wadda mataimakin shugaban yayi wa jagoranci. An yi zargin cewa Atiku Abubakar ya taimakawa abokan huldarsa da abokan siyasarsa da wannan kudin.

Mataimakin shugaban ba ya kotu jiya talata, an kuma daga wannan kara har sai 16 ga watan Nuwamba.

Wani kakakin mataimakin shugaban, Adeolu Akande, ya ce ai wannan kotu ta musamman ba ta ma da hurumin sauraron wannan kara tun da shi Atiku Abubakar ya riga ya shigar da kara a gaban wata babbar kotu a Abuja game da wannan tuhuma da ake yi masa. Akande ya kara da cewa, "...ai Atiku Abubakar ya kalubalanci shawarar Atoni janar ta gabatar da wannan batu a gaban kotu ta musamman ta tabbatar da da’ar jami’an gwamnati. A bisa tsarin shari’a, kotun ta musamman ba zata iya fara sauraron wannan batu ba har sai babbar kotu ta yanke hukumci a kan halalcin wannan tuhuma. A saboda haka matsayinmu shine a shirye muke mu bi sawun wannan batu a babbar kotu, mu tabbatar da cewa an kare tsarin doka."

Irin wannan mataki na gurfanar da jami’in gwamnatin dake kan mulki a gaban kotu dai ba a taba ganin irinsa a Nijeriya ba, kuma yana da alaka da rikicin da ya kaure a bainar jama’a a tsakanin shugaba Obasanjo da mataimakin nasa. Wannan rikici nasu ya kara muni a farkon wannan shekara a lokacin da shi mataimakin shugaba Atiku Abubakar ya fito a fili ya jagoranci wani gangami na yaki da kokarin da aka yi na yin gyara ga tsarin mulki domin a kyale Obasanjo yayi Tazarce.

Akande, ya ce wannan tuhuma da ake yi wa Atiku, ba wata aba ba ce illa munakisar siyasa ta son zuciya. Akande ya ce, "...idan ka dubi yadda suka tashi gadan gadan a kan wannan batu, cikin makonni biyu an gudanar da bincike, majalisar zartaswa ta tarayya ta yi zama a kai, an rubuta cikin takardar shawarwarin gwamnati, an kuma gabatar gaban kotu ta musamman. Duk wannan cikin kwanaki goma, bai taba faruwa ba a tarihin Nijeriya. Kuma dukkan bayanai sun nuna cewa gwamnati ba ta yi hasarar ko kwabo ba, babu wata hujjar da aka bayar, amma ga su nan suna kai gwauro da mari. Wannan duk yunkuri ne kawai na hana mataimakin shugaba Atiku Abubakar yin takara a zaben shugaban kasa na 2007."

’Yan Nijeriya da dama suna fargabar cewa wannan kai ruwa rana da ake yi a tsakanin Obasanjo da mataimakinsa zai gurgunta kasar kafin zaben da zai kai ga mika mulki na farko daga hannun wata gwamnatin dimokuradiyya zuwa hannun wata. Nijeriya, wadda ta fi kowace kasa samar da man fetur a Afirka ta koma ga mulkin dimokuradiyya shekaru 7 da suak shige a bayan da sojoji suka shafe shekaru fiye da 30 suna mulki kusan ba tare da tsinkewa ba.

XS
SM
MD
LG