Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

"yan kallo na tsoro kadda yaki ya kaure a Somalia


“Yan kallo suna bayyana fargaban cewa karuwar tankiya da ake samu tsakanin gwamnatin rikon kwaryar kasar dake samun goyon bayan gwamnatin Ethopia da kuma ‘yan kishin Islamar kasar tana kaiwa wani matsayi inda wata kila dakyar a kaucewa barkewar yaki. Tun da fari a wannan wata, ‘yan kishin Islamar suka ayyanar da yaki a kan kasar Ethopia dake makobtaka dasu in da suke zarginta da laifin tura sojojinta su taimaki sojojin gwamnatin wadanda suka dan kwace ikon garin Buur Hakaba, garin da ada yake hannun mayakan sai kai masu kishin Islama.

Tun daga wancan lokaci an sha samun rahotannin arangama tsakanin mayakan sa kai masu goyon bayan gwamnati da kuma mayakan ‘yan kishin Islamar a garin Kismayo mai tasoshin jirajen ruwa da kuma kusa da garin Bu’aale mai tazaran kilomita dari 3 da 50 daga kudancin garin Baidoa inda gwamnatin rikon kwaryar kasar ke da zama. Dangantaka tsakaninsu ta dada sukukucewa a ranar Lahadi lokacin da mazauna garin Dinsor dake kudancin kasar suka bada rahoton cewa sojojin kasar Ethopia dauke da makamai sun rufawa sojojin gwamanti baya inda suka kwace garin. Shugabannin kotunan Islamar kasar a birnin Mogodishu sun kwace ikon birnin daga hannun shugabannin bangarorin kasar watanni 4 da rabi da suka wuce sunce yadda sojojin gwamnatin suka shiga garuruwan dake hannunsu wani mataki ne na keta haddin sharradin zagayen tattaunawar zaman lafiyar da suka cimma a birnin Khartoum tsakaninsu.

Yarjejeniayr tasu ta amince da kasancewar kowa daga cikinsu a kasar Somalia kuma sun dauki alkawari akan ba zasu kaiwa juna hari ba.

To amma wani mai fashin bakin siyasar yankin dake da zama a birnin Nairobin kasar Kenya Matt Bryden ya ce gwamantin rikon kwaryar kasar da kuma gwanatin Ethopia sun zargi kotunan islamar kasar Somalia da laifin alaka da kungiyar Alka’ida, kuma suna kara tsusa tsoro azukata ta yadda suke kokarin kara kama yankunan sassan kasar. Ya ce wadannan kotuna suna kara fadada yankunan su kuma sun tura sojojinsu su mai da martini ga tura soja da kasar Ethopia ta yi zuwa kusa da Somalia. Don haka akwai hatsarin gaski ayanzu, a lokacin da wadannan sojojin suka samu, suka kutsa kai zuwa kusa da juna, anan ne za aga tashin hankali tsakaninsu. Watakila da gangan za su tsokani juna.

A kwai hatsari ganin tashin hankali nan bada jimawa ba. Bryden yace hanya daya da za’abi wajen warware wannan cijewar itace ta jami’an kungiyar ‘yan kishin Islamar da kuma na gwamantin rikon kwaryar kasar su sake komawa teburin shawarwari zauren shawarwari da kungiyar tarayyar larabawa ta shirya a birnin Khartoum, Ya ce yana jin hakan abune na hanzari da ake bukata bangarorin biyu su shirya yadda zasu tinkari zagayen tattaunawar kawo zaman lafiya da za ayi nan gaba a ranar 30 ga wannan wata na Oktoba.

XS
SM
MD
LG