Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da Japan Zasu Hada Kai...


Amurka da Japan sun yi alkawarin yin aiki tare wajen aiwatar da takunkumin da aka kafawa Koriya ta Arewa a bayan da ta yi gwajin makamin nukiliya a makon jiya.

A taron da suka yi da 'yan jarida bayan wata ganawa a birnin Tokyo, sakatariyar Harkokin Wajen Amurka, Codoleezza Rice, da takwaranta na Japan, Taro Aso, sun ce zasu yi aiki tare domin a tabbatar an aiwatar da takunkumi mai tsauri da aka sanyawa Koriya ta Arewa, wanda zai haramta duk wata harkar cinikin da zata taimakawa shirin makamanta na nukuliya.

‘Yan adawar siyasar Japan basa goyon bayan amfani da dakarun kasar, domin taimakawa Amurka wajen bincikar jiragen Korea ta Arewa wadanda ka iya daukar kayan da takunkumin ya haramta.

Amma Rice tace ba wai so Amurka take ta kara tsananta rikicin da ake ciki ba, ta hanyar yin wannan bincike, abinda babu shakka Koriya ta Arewa zata dauka a matsayin tsokana. Ranar talatar da ta gabata dai Pyonyang tace ta dauki wannan mataki na majalisar Dinkin Duniya a matsayin ayyana yaki a kanta, kuma zata dagargaza duk kasar da ta keta haddinta.

Wannan bincike dai zai zo ne karkashin shirin hana yaduwar makaman kare dangi, wanda aka fara a shekara ta 2003, wanda yake kokarin hana bazuwar makaman kare dangi, ko sayar dasu da kayan gyaransu. Fiye da kasashe 75, cikinsu har da Japan suke da hannu a wannan shiri wanda aka fi fuskantar Koriya ta Arewa da shi.

Gobe alhamis Rice da Aso zasu je Seoul domin tattaunawar kasashe uku, da Ministan Harkokin Wajen Koriya ta Kudu, Ban Ki-moon. Daga nan kuma sai Rice ta wuce zuwa Beijing da Moscow. Ana ganin China tana da muhimmiyar rawar da zata taka wajen tabbatar da nasarar wannan takunkumi da kwaminitn tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya amince dashi bai daya.

Amma Beijing tana inda-inda a kan yadda za a lakabawa tsohuwar kawarta takunkumin. Tattalin arzikin Koriya ta Arewa dai, ya dogara ainun a kan kasar China, wadda ke kai mata abinci da makamashi.

XS
SM
MD
LG