Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Gwamnatin Somaliya Sun Janye Daga Wani garin Da Suka Kwace Ranar Asabar


Shaidu a kudancin Somaliya sun ce sojojin gwamnati sun janye daga wani garin da suka kwace a hannun ’yan kishin Islama ranar asabar da ta shige.

Ba a san dalilin da ya sa sojojin na gwamnati suka janye daga garin Bur Hakaba ba

Wasu mazauna garin sun gudu a saboda suna fargabar cewa za a sake gwabza fada a tsakanin sojojin gwamnati da sojojin sa kai masu yin biyayya ga kotunan Islama na Somaliya.

Sassan biyu sun gwabza a wani garin dabam mai suna Buale a kudancin kasar jiya lahadi. Dukkan sassan biyu kuma suna ikirarin cewa sune ke rike da garin wanda yake arewa da birnin Kismayo mai tashar jiragen ruwa.

A cikin ’yan kwanakin nan, gwamnatin rikon kwarya ta Somaliya ta fara kalubalantar mamaye kudancin kasar da masu kishin Islama ke yi. Masu kishin Islamar suna rike da wasu muhimman garuruwa da birane, ciki har da Mogadishu, babban birnin kasar.

An ce gwanatin tana samun tallafi daga sojojin kasar Ethiopia makwabciyarsu. A yau wani shugaban kungiyar kotunan Islama a Somaliya, Sheikh Sharif Sheikh Ahmed, yayi kira ga ’yan ethiopia da su tayar da kayar baya ma gwamnatin firayim minista Meles Zenawi.

XS
SM
MD
LG