Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sudan ta kori Manzon MDD daga kasarta


Manzon MDD a kasar sudan Jan Pronk ya tashi daga kasar yana kan hanyarsa ta zuwa birnin NY bayan da gwamnatin Sudan ta koreshi daga kasar. A gobe larabane Mr Pronk zai sauka a Helkwatar MDD domin ya gana da kakakin MDD Kofi Annan wanda ya bayyana alwashinsa bisa kwarewar wannan manzo na MDD.

Wani mai magana da yawun MDD Stephen Dujarric ya jadda cewa Pronk zai ci gaba da ayyukansa na wannan mukami da aka ba shi kuma yanzu ya fita daga birnin Khartoum ne domin ya sake tuntubar MDD, amma ba wai yana aiki ne da umurnin gwamnatin Sudan ba.

Amma mai maganma da yawun ma’aikatar harkokin wajen Sudan, ya ce an kori manzon na Majalisar Dinkin Duniya ne saboda muguwar manufarsa akan gwamnatin Sudan da kuma sojojinta. Pronk ya rubuta a wani dandalin gizo-gizo nasa a makon jiya,cewa sojojin‘yan tawaye a yankin Darfur sun baiwa sojojin gwamnatin Sudan kashi har sau biyu saboda haka sunji kunya ainun.

XS
SM
MD
LG