Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Iraqin zasu iya karbar ragamar harkar tsaron kasar baki daya nan da shekara daya zuwa  daya da rabi


Wani janar na sojojin Amurka a Iraqi yace sojojin Iraqin zasu iya karbar ragamar harkar tsaron kasar baki daya nan da shekara daya zuwa shekara daya da rabi.

Janara George Casey ya fada a taron manema labaru a Iraqi yau cewa Amurka zata maida hankalinta wajen rage yawan dakaraunta a Iraqi,amma yace zai bukaci Karin sojoji idan akwai bukatar haka. Haka shima a taron na manema labaru jakadan Amurka a Iraqi Zalmay Khalizad yace shugabannin Iraqi sun amince da tsara lokaci na cimma burin, kamar inganta tsaro da tattalin arziki.

Jami’an Amurkan duka biyu sun zargi kasashe dake makwabtaka da Iraqin Syria da Iran da laifin goyon baya masu gwagwar maya.

XS
SM
MD
LG