Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Yace Hakurin Amurka Yana Da Iyaka Game Da Yakin Iraqi


Shugaba Bush ya ce hakurin da Amurka zata iya yi da yakin da ake yi a Iraqi takaitacce ne, amma kuma ya ce Amurka ba zata matsa lamba fiye da kima kan shugabannin Iraqi na su maido da kwanciyar hankali a kasar ba.

A lokacin da yake zantawa da ’yan jarida larabar nan a fadarsa ta White House, shugaban ya lashi takobin cewa sojojin Amurka zasu ci gaba da zama a Iraqi, amma kuma ya ce zasu ringa sauya dabarunsu domin takalar abokan gaba.

Shugaban ya takali rashin goyon bayan da Amurkawa ke kara nunawa da yakin na Iraqi, yana mai nanata cewar Amurka tana da tsari ko dabarar tabbatar da nasara a Iraqi. Ya ce tabbatar da kwanciyar hankali a kasar yana da matukar muhimmanci ga tsaron Amurka.

Mr. Bush ya ce kamar Amurkawa da yawa, shi ma bai gamsu da halin da ake ciki a Iraqi ba, amma kuma har yanzu yana nan daram a kan kudurin goyon bayan manufar wannan yaki.

Wannan ganawa da ’yan jaridar da shugaban yayi ta zo ne ana saura makonni biyu a gudanar da babban zaben ’yan majalisar dokokin tarayya a fadin Amurka, zaben da batun yakin Iraqi ya zamo mai muhimmanci a cikinsa.

XS
SM
MD
LG