Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Iraq an kashe sojojin Amurka guda biyar a lardin Anbar dake yammacin kasar


Rundunar sojojin Amurka a Iraqi ta ce an kashe sojojin Amurka guda biyar a lardin Anbar dake yammacin kasar, abinda ya kawo adadin sojojin Amurka da aka kashe a wannan wata zuwa casa’in da shida.

Wannan shine adadi mafi yawan na sojojin Amurka da aka kashe cikin wata guda a wannan shekara. Wani kakakin sojojin na Amurka a Bagadaza ya ce sojojin sun rasa rayukansu ne a yayin da suka ci gaba da farmakin maido da birnin Ramadi dake lardin na Anbar karkashin ikon hukumomin Iraqi.

Kakakin, Janar William Caldwell, ya ce tun bayan da aka kammala azumin watan Ramadan, tashin ahnkali ya ragu a Bagadaza, amma kuma ba a san ko lamarin zai dore a haka ba tukuna. haka kuma a yau alhamis, ’yan sandan Iraqi suka ce ’yan bindiga a Bagadaza sun kashe ’yan sanda akalla biyar suka raunata wasu goma.

XS
SM
MD
LG