Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Girka Sojojin Ruwa Na Kawance Suna Sintiri A Tekun Farisa


An sanya sojojin ruwa na kawance dake tekun Farisa cikin damara domin takalar barazanar ta'addanci kan cibiyoyin mai a Saudi Arabiya da Bahrain.

Rundunar mayakan ruwan Britaniya ta bayar ad sanarwa a yau Jumma'a tana yin kira ga jiragen ruwan dake safara a cikin tekun da su sanya idanu ko zasu ga wasu jiragen ruwa ko kuma take-take na ba-sabam ba. Jami'ai suka ce ana gudanar da ayyukan safarar man fetur a yankin kamar yadda aka saba.

Jami'ai suka ce an kara matakan tsaron ne a dalilin wata barazanar da kungiyar al-Qa'ida ta yi kan cibiyoyin lodin mai dake tekun Farisa a watan da ya shige.

Karin matakan tsaron sun hada har da kara sanya idanu a kan tashar lodin mai cikin teku mafi girma a duk duniya, watau tashar Ras Tamura ta kasar Saudi Arabiya.

XS
SM
MD
LG