Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sultan Muhammadu Maccido Na Cikin Wadanda Suka Rasu A Hatsarin Jirgin Sama A Abuja


Mutane kimanin dari daya suka rasa rayukansu, ciki har da Sarkin Musulmin Nijeriya, Sultan Muhammadu Maccido.

Jirgin ya fado kasa, ya kama da wuta jim kadan a bayan tashinsa daga babban birnin tarayya, Abuja, yau lahadi.Gidan rediyon Nijeriya ya ce akwai hadarin ruwan sama a lokacin da jirgin yake tashi.

'Yan jarida da suka je su inda jirgin yayi hatsari, sun ga gawarwakin mutanen da suka kone warwatse a kasa da kuma a cikin garewanin jirgin dake cin wuta. Kafofin labarai na Nijeriya suka ce mutane hudu ko biyar sun kubuta da rayukansu.

Wannan jirgi na wani kamfanin safarar jiragen saman Nijeriya mai zaman kansa ne da ake kira "Aviation Development Corporation" ko kuma ADC a takaice. Jirgin ya tashi ne zai doshi Sakkwato a yankin arewa maso yammacin Nijeriya.

Shugaba Olusegun Obasanjo na Nijeriya ya mika ta'aziyyarsa, ya kuma bayar da umurnin da a gudanar da cikakken bincike.

A cikin wannan jirgin dai har da sarkin Musulmi, Sultan Muhammadu Maccido, wanda shine shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Nijeriya. Har ila yau shi ne babban basarake a arewacin Nijeriya. Kimanin rabin mutane miliyan 130 na Nijeriya Musulmi ne.

Gwamna Attahiru Bafarawa na Jihar Sakkwato ya bayyana zaman makoki na tsawon kwanaki biyar.

Sauran wadanda ke cikin jirgin sun hada har da dan sarkin Musulmi, Badamasi Maccido, wanda dan majalisar dattijan Nijeriya ne, da wani dan majalisar dattijan mai suna Sule Yari Gandi, da mukaddashin gwamnan Jihar Sakkwato da kuma Abdul-Rahman Shagari, dan tsohon shugaban Nijeriya Alhaji Shehu Shagari.

XS
SM
MD
LG