Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bangarorin Kasar Kwango-Ta-Kinshasa Suna Zargin Juna Da Magudi A Zaben Shugaban Kasa


Sassa masu adawa da juna a zaben fitar da gwani na shugaban kasa da aka yi a Kwango-ta-Kinshasa sun zargi da juna da laifin ha’inci. Wadannan zarge-zarge su na zuwa ne a daidai lokacin da aka fara kidaya kuri’un da aka kada a zaben na jiya lahadi a wannan kasa dake tsakiyar Afirka.

Magoya bayan shugaba Joseph Kabila sun zargi abokin adawarsa, watau tsohon madugun ’yan tawaye Jean-Pierre Bemba, da laifin gudanar da abinda suka kira wani gagarumin aikin magudin zabe a yankunan yammaci da tsakiyar kasar inda yake da tasiri.

Su kuma magoya bayan Mr. Bemba sun zargi magoya bayan shugaban da kokarin sayen kuri’u da kuma yin amfani da takardun kuri’un da aka riga aka zabi shugaban a jiki a duk fadin kasar.

Duk da wannan tankiya jami’an Kwango sun ce an gudanar da zaben na jiya lahadi lami lafiya im ban da a wasu wurare kalilan. Jami’ai sun ce wani sojan da a bisa dukkan alamu ya bugu da barasa, ya kashe ma’aikatan zabe biyu yau litinin a kusa da Bunia, babban birnin lardin Ituri. Jami’an suka ce gungun mutanen da suka fusata da wannan tashin hankalin sun kai farmaki kan rumfunan zabe da dama.

XS
SM
MD
LG