Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar 'yan Kishin Islama na kasar Somalia  sunce ba za su  shiga taro.....


Ayarin ‘yan kishin Islama na kasar Somaliya sunce zaman tattaunawar kawo zaman lafiya domin kaucewa yakin basasa a kasar da aka shiryi yi tsakanin bangarorin kasar ba zata samu ba muddin dai injisu, kasar Ethopia tana shiga musu kasa.

A kasar Sudan inda aka shirya zaman taron jiya Litinin, wakilan kungiyar su 16, sun sake neman sojojin Ethopia akan su fice musu daga cikin kasa kafin a kaiga shiga zauren taron. Wakilan gwamnatin rikon kwaryar kasar Somalia basu je wajen taron da wuri ba sai can da marece. Bangarorin biyu sun gana a kebe da jami’an diplomasiyya domin nuna fatarsu ta ganin cewa za’a zauna shawarwari a yau Talata.

Anan birnin Washington kuma gwamnatin Amirka ta bayyana gujewa taron da masu goyon bayan kotunan Islamar kasar suka yi a matsayin wani abin takaici, kana ta roki duk bangarorin akan su halarci taron da za’a fara a yau Talata. Amirka dai ta zargi magoya bayan kotunan Islamar da laifin baiwa ‘yan kungiyar Alqaida mafaka.

Su dai masu goyon bayan kotunan Islamar kasar suna kukar cewa akwai sojojin kasar Ethopia a garin Baidoa helkwatar gwamnatin rikon kwaryar kasar. Ita kuma Ethopia ta lashi takwabi akan za ta kare lafiyar gwamnatin rikon kwaryar wacce bata da wani karfin kirki a wajen garin Baidoa.

XS
SM
MD
LG