Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnati Da 'Yan Tawayen Uganda Sun Sabunta Yarjejeniyar Tsagaita Wuta


Gwamnatin Uganda da kungiyar ’yan tawayen “Lord’s Resistance Army” sun sake sabunta yarjejeniyar tsagaita wuta mai tarihi, matakin da ya karfafa fatar gudanar da tattaunawar cimma zaman lafiya da nufin kawo karshen mummunan yakin basasar da aka shafe shekaru ashirin ana gwabzawa.

Sassan biyu sun bayar da sanarwar cimma sabuwar yarjejeniyar yau laraba a Juba, babban birnin yankin kudancin Sudan, inda suke tattaunawa. An yi aiki da yarjejeniyar da sassan biyu suka rattabawa hannu a watan Agusta duk da cewa sun yi ta zargin juna da laifin keta ta.

A watan da ya shige wancan yarjejeniya ta kammala aiki.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ce ’yan tawayen sun sake daukar alkawarin tattaruwa a wasu cibiyoyi biyu na ’yan babu-ruwanmu a kudancin Sudan, yayin da za a ci gaba da tattaunawar neman zaman lafiya.

Shekaru ashirin da aka yi ana fada ya lalata yankin arewacin Uganda, ya kashe dubban mutane, yayin da ya sa wasu fiye da miliyan daya suka koma sansanonin ’yan gudun hijira. Mutane fiye da dubu dari uku sun koma gidajensu cikin ’yan watannin nan a saboda tsagaitawar fada.

XS
SM
MD
LG