Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wuraren kada kuri’a na farko sun bude kofofinsu a zaben Amurka


Wuraren kada kuri’a na farko sun bude kofofinsu a zaben Amurka wadda zai tabbatar da abubuwa da dama ciki harda wace Jamiyya ce zata yi jagorancin Majalisa.A kuri’un neman ra’ayin jama’a na baya bayan nan,ya nuna cewa jamiyyar hamayya ta The Democrat sai ta yiwu ta sami rinjaye kujerun da take bukata a majalisar wakilai,amma yana da wuya ayi hasashen jamiyyar da zata sami rinjayen rike Majalisar dattijai saboda kusan a wasu mazabun ‘yan takarar suna kusan kunnen doki.

Zaben na yau talata ya hada da zaben gwamnoni a jihohi da dama, da kuma wasu bukatu da masu zabe zasu kada kuri’u a kansu.Shugaba Bush ya kada kuri’arsa a garin Crawford Texas inda yake da gida,kamin ya dawo fadar White House.Ranar Litinin yayi kamfel a jihohi dake kudancin Amurka, Florida Arkansas,da kuma Texas.

Mr. Bush Ya bukaci dukkan masu kada kuri’a su zabi Jamiyyar Republican idan suna mutunta tsaron lafiyarsu da kuma biyan karancin haraji. Koda yake shugaba Bush baya takara a wannan zabe yana kamfel sosai a madadin ‘yan Jam’iyyar Republican dake takara.

XS
SM
MD
LG