Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Hamayya A Nijeriya Sun Bukaci Da A Binciki Wani Babban Mashawarcin Shugaba Obasanjo


Shugabannin hamayya a Nijeriya su na matsawa gwamnati lamba a kan ta binciki tuhumar da aka yi ma wani babban mashawarcin shugaba Obasanjo ta kokarin batar da sawun kudaden haramun.

Wannan bukata ta su tana da nasaba da tuhumar Andy Uba da laifin fasa kwabrin kudi da aka yi a nan Amurka, labarin da ya fara kunno kai ranar talata a Nijeriya.

Watanni da dama da suka shige, wata kotu a nan Amurka ta tuhumi Andy Uba da laifin shigowa Amurka da tsabar kudi har dala dubu dari da saba'in, kimanin Naira miliyan ashirin da biyu, a cikin wani jirgin saman shugaban Nijeriya ba tare da ya bayyanawa hukumomi cewar yana dauke da wannan kudin ba. Wannan lamari ya faru a 2003. Wata budurwar Andy Uba a nan Amurka ta yi amfani da kudin ta sayi wata motar alatu ta aika masa a Nijeriya. Har ila yau ta yi amfani da kudin ta sayi kayayyakin noma domin gonar shugaba Obasanjo a Otta.

Daga baya, Andy Uba ya biya tara a gaban kotun, ya kuma yarda ya mikawa hukuma dala dubu 26, kimanin Naira miliyan uku da dubu dari uku, daga cikin wannan kudi da yayi fasa kwabrinsa.

Kafofin labarai suka ce Uba yayi tayin yin murabus daga mukaminsa na mai bai wa shugaba Obasanjo shawara. Amma kuma jami'an Nijeriya su na musanta muhimmanci ko munin wannan lamari, su na masu fadin cewa an murda gaskiyar labarin.

XS
SM
MD
LG