Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sanata George Allen Dan Jam'iyyar Republican Daga Jihar


Sanata George Allen dan jam’iyyar Republican, ya mika wuya, ya yarda cewar an kayar da shi a zaben kujerar karshe ta majalisar dattijai da ake jiran sakamakonta, matakin da ya bai wa jam’iyyar Democrat ragarmar jagorancin dukkan majalisun dokoki biyu na tarayya.

Sakamakon zaben majalisar dattijai a Jihar Virginia ya nuna cewa abokin takarar Allen a jam’iyyar Democrat, Jim Webb, yana gaba amma da rata maras yawa, kuma an tsammaci za a sake kidaya kuri’u. Amma Allen ya yanke shawarar zai mika wuya kawai ya yarda da kayen da aka yi masa. Wannan nasarar ta Jim Webb tana nufin cewa a yanzu kowacce daga cikin jam’iyyun Democrat da Republican tana da kujeru 49 a majalisar dattijai mai kujeru 100, amma kuma wasu sanatoci biyu ’yan Indipenda sun yi alkawarin yin aiki tare ne da ’yan jam’iyyar Democrat. Tun kafin nan ’yan jam’iyyar ta Democrat sun samu rinjaye a majalisar wakilai. Wannan zai zamo karo na farko da ’yan Democrat zasu jagoranci dukkan majalisun guda biyu a cikin shekaru 12.

Yau alhamis a fadar White House, shugaba Bush ya taya ’yan Democrat murnar nasarorin da suka samu, ya kuma yi kira ga dukkan jam’iyyun da su ajiye bambancinsu a gefe guda su yi aiki tare kan batutuwa masu muhimmanci ga Amurkawa. Har ila yau Mr. Bush ya gana da shugabannin Democrat a majalisar wakilan tarayya, Nancy Pelosi da Steny Hoyer.

Pelosi tana shirin zamowa macen farko da zata jagoranci majalisar wakilan tarayya a tarihin Amurka. A gobe jumma’a Mr. Bush zai gana da shugabannin Democrat a majalisar dattijai.

XS
SM
MD
LG