Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane kusan hamsin suka mutu a somalia inji kungiyoyin agaji


Kungiyoyin agaji na kasashen duniya sun ce ambaliyar ruwa a yankin kudancin Somaliya ta kashe mutane kusan hamsin, ta kuma sa wasu fiye da dubu uku suka rasa gidajensu. Maâ aikatan agaji suka ce ambaliyar ruwan ta lalata garin Jowhar kewaye a yankin Shabelle na tsakiyar kasar. Wani jamiâ'in kungiyar agaji ta CARE, david Gilmore, ya ce ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi kwana da kwanaki ana juyewa, ya sa kogin Shabelle ya cika ya batse, ya malale kauyuka 170 da kadada dubu daya da dari biyar ta gonaki. Har ila yau, ruwan sama kamar da bakin kwarya ya haddasa ambaliya a wasu sassan yankin Gedo dake bakin iyaka da kasashen Ethiopia da Kenya. Mazauna yankin suka ce kogin Juba ya batse jiya laraba da safe, ya kashe mutane kimanin 10, wasu dubbai kuma suka arce zuwa yankunan dake kan tudu.

XS
SM
MD
LG