Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jiragen saman yakin Amirka suna fara lugujen wuta kan anguwannin 'yan shi'a a Bagadaza......


Shedun gani da ido da kuma jami’ai a birnin Bagadazan a Iraq sunce sojojin Amirka sun kai wani farmaki daga sama akan wata anguwa ta ‘yan shi'a inda suka kashe akallan mutane 5.

Wadansu rahotanni da suke fitowa daga birnin Bagadaza sunce watakila hare haren jiragen saman yakin Amirkan akan wata tsangaya ta ‘yan shia mai suna Shula sun yi sanadiyyar mutuwar wajen 9. Wani kakakin rundunar sojin Amirka a birnin yace ba zai ce uffam ba akan wadannan hare haren da suke kaiwa. Jiya Litinin ‘yan sanda sun gano gawarwakin mutane 46 a ciki da kewayen birnin Bagadaza.

Mafi yawa daga cikin wadannan gawarwaki an gana musu azaba kafin su mutu a lokacin wata arangamar jinsin addini. Haka kuma a cikin birnin Bagadazan, jami’an ‘yan sandan birnin sunce, wata motar daukar kaya dauke da bama baman kunar bakin wake ta ci karo da wata motar safarar mutane a wata Anguwar ‘yan shi’a a gundumar Shaab inda ta kashe mutane 11. Haka kuma wani bam da ya tashi a birnin ya kashe sojojin Amirka 2.XS
SM
MD
LG