Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma’aikatar Tsaron Amurka ta Pentagon, tana duba yiwuwar kafa wata runduna ta musamman kan Afrika


Ma’aikatar Tsaron Amurka ta Pentagon, tana duba yiwuwar kafa wata runduna ta musamman kan Afrika, a cikin tsarin sojinta, daga shekara mai zuwa. Wani mai Magana da yawun Ma’aikatar ta Pentagon, yace tuni har an kafa wani kwamitin tsare-tsare, mai wakilai daga sassa dabam-dabam, don tsara yadda wannan runduna ta Africa zata kasance.

Manufar wannan runduna, wadda har yanzu bata sami amincewar Shugaba Bush ba, shine samara da hanya mai sauki ta aiwatar da aiyukan tsaro na hadin guiwa a Africa.

Kakakin na Peantagon yace ma’aikatar tana duba ingantattuin hanyoyin magance matsalolin ta’addanci, da kuma kyautata ceton rayuka da aikin jin kai, sa’annan kuma da tabbatar da zaman lafiya Africa. Kwamitin Tsare-tsaren dai yana da har zuwa farkon shekara mai zuwa, don gabatar da shawrwarinsa.

XS
SM
MD
LG