Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sugabannin kungiyar Kasashen APEC sunce zasu kara karfafa hanyar kasuwanci tsakaninsu..


Jiya, Lahadi Shugabannin kungiyar habaka cinikayya da tattalin arziki na yankin Asiya da Pacifika sun dau alkawari akan zasu ciyar da harkokin cinikaiyya gaba a tsakaninsu sannan zasu yaki da ayyukan ta’addanci, shugabannin sun bayyana matukar damuwa game da Nukiliyar kasar Koriya ta Arewa.

Shugabannin sun bayyana haka ne a jawabin bayan taron kungiyarsu ta APEC, na shekara shakera da suka kamala jiya Lahadi, abirnin Hanoi na kasar Vietnam. Shugaban kasar Vietnam Nguyen Minh Triet, ya karanta wani jawabi a birnin Hanoi din inda yake bayyana gwajin makaman Nukiliya da kasar Koriya ta Arewa tayi a watan Oktoba a matsayi "barazana a fili". Kana ya roki kasar akan ta rike alkawarin dauka na daina kera amakaman Nukiliya. Duk da haka batun kasar Koriya ta Arewa, bai fito cikin bayanan karshen taro da kungiyar ta APEC ta bayarba.

Jami’ai a wajen taron sunce koda yake shugabannin sun hada kai wajen bayyana damuwarsu game da gwajin Nukiliyar ba, sun kasa tsaida shawara bisa yadda zasu bayyana damuwarsu. Bayanan karshen taron kungiyar sun nuna cewa shugabannin sunyi gargadin cewa, za’a fuskanci wata matsalar tattalin arziki idan har zagayen taron kasa da kasa na habata harkokin cinikayya na garin Doha bai tsinana komai ba. Kungiyar dai ta yi alkawari sake farfado da taron wanda ya tashi baram-baram a watan Yuli bayan da aka sami sabanin ra’ayi agame da batutuwa da suka shafi cinikayyar akan albarkatun gona.

XS
SM
MD
LG