Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Syria  da Iraqi sun dawo da dangantakar diplomasiyya, bayan shekaru kusan  25


Syria ko Sham, da Iraqi sun dawo da dangantakar diplomasiyya, bayan shekaru kusan 25 ana zaman doya da manja. Hukumomin Iraqi sunce yau talata aka mayar da huldar diplomasiyyar a yayin wata ziyara da Ministan harkokin wajen Syria, Walid Muallim ya kai birnin Bagadaza. Wani mai Magana da yawun Majalisar Tsaron Amurka, Gordon Johndroe, kirayi Syria da ta nuna da gasket take yi, ta hanyar hana mayakan sa kai shiga kasar Iraqi, ta kan iyakokinsu.

Ya kara da cewa dama kullum Amurka na na godon kasashen dake makwabtaka da Iraqin su taimaka mata. A wani labarin makamancin wannan, jami’an Iraqi sunce Shugaba Jalal Talabani zaiyi wani tattaki zuwa birnin Tehran rananAsabar domin tattaunawa da Shugaban Farisa, ko kuma Iran, Mahmud Ahmedinejad. Saidai jami’an sun musanta bayanan dake cewa Shugaba Bashar Al-Asad na Syria zai shiga cikin tattaunawar.

A halin da ake ciki kuma, yau Talata aka kashe mutum uku, a wani hari da aka kai unguwar Sadr City ta Birnin Bagadaza. Jami’an sojin Amurka sunce a yau din dai, an kame mutun bakwai, daya daga cikinsu kuma ana kyautata zaton yana da masaniyar inda sojan Amurkan nan da aka sace yake.

XS
SM
MD
LG